Rundunar ’yansandan Jihar Jigawa, ta kama karin mutane 82 bisa zargin sace kayan jama’a a lokacin zanga-zangar yunwa a jihar.
Kakakin rundunar ’yansandan, DSP Lawan Shiisu, ya ce an kama su ne a ranar Asabar da Litinin.
- Sojoji Sun Kama Sojan Da Ya Kashe Mai Zanga-zanga A Kaduna
- Gwamnan Bauchi Ya Sassauta Dokar Hana Zirga-zirga A Katagum
Wannan ya kawo adadin mutanen da aka kama tun daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 294.
Daga cikin mutane 212 da aka kama a baya, ’yansanda sun gano kayayyaki kamar buhun taki 303 da babura 50 da Keke Napep uku da kekuna 12 da kujeru tara da buhun shinkafa biyu da kayan ofis.
Shiisu, ya ce 37 daga cikin mutanen 212 da aka kama an kama su ne saboda fasa kayan gwamnati a ranar Asabar.
Ya ce wasu mutanen sun shiga gidan baki da gidan gona na Sanata Babangida Hussaini, inda suka sace kayayyakin miliyoyin kudi.
A ranar Litinin, an kara kama mutane 45 a wurare daban-daban kuma ’yansanda sun gano kayayyaki kamar buhun dawa 30 da buhun taki 94 da babura biyu da sauran kayayyaki.
An gurfanar da mutane 195 daga cikin wadanda ake zargin a gaban kotu.
Yanzu haka al’amura sun fara daidaita a jihar ba tare da rahoton samun tashin hankali ba.