Jami’an hukumar ‘yansandan jihar Bauchi sun samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa kai wajen kashe wani ɗan Achaɓa, Dauda Manu, ɗan shekara 25, mazaunin unguwar Buba da ke Fulata Lanzai, a cikin ƙaramar hukumar Darazo ta jihar Bauchi.
An tsinci gawar Manu ne a ƙauyen Doshe da ke kusa da Darazo tare da munanan raunuka.
- Kamfanin Apple Ya Sanar Da Zuba Sabon Jari A Fannin Samar Da Makamashi Mai Tsafta A Sin
- Dokar Ta-ɓaci A Ribas: Gwamnonin PDP Sun Ƙalubalanci Hukuncin Tinubu A Kotun Ƙoli
A wata sanarwar manema labarai da kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewar kafin rasuwar Manu an yi masa gani na ƙarshe ne ranar 4 ga watan Maris ɗin 2025 sa’ilin da ya goyo wasu mutane biyu da ba tantance ko su waye ba a kan Mashin ɗinsa kirar Boxer.
“Lokacin da aka samu rahoton faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagoranci babban baturen ɗansanda (DPO) sun ziyarci wurin inda suka ɗauki gawar zuwa babban asibitin Darazo, a nan ne likita ya tabbatar da mutuwarsa,” Wakil ya shaida.
Yayin da bincike ya ci gaba da gudana, a ranar 20 ga watan Maris, ‘yansanda suka kama Yau Buba, ɗan shekara 25 mazaunin ƙauyen Minchika da ke Darazo a jihar Gombe tare da Mashin ɗin da aka sace daga hannun ɗan Achaɓan da aka kashe.
Wakil ya ƙara da cewa, a yayin da ake masa tambayoyi, shi Yau Buba ya bayyana da kansa cewa ya sayi Babur ɗin ne a hannun wani mutum mai shekaru 22 a duniya wato Buba Muhammadu, da suke ƙauye ɗaya a kan kuɗi Naira dubu ɗari biyu da hamsin ₦250,000.
Muhammadu shi ma an kamashi a ranar 21 ga watan Maris.
A halin da ake ciki an mayar da kes ɗin zuwa sashin kula da manyan laifuka (SCID) domin zurfafa bincike, “Idan aka kammala bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu,” PPRO ya tabbatar.
Har-ila-yau, rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta sake jaddada aniyarta na dakile ayyukan ta’addanci da wanzar da zaman lafiya da kare rayukan da dukiyar jama’a a fadin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp