Rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi ta kama wasu mutum hudu da ake zargi da lalata wata na’urar taransifoma a makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke Bunza a Karamar Hukumar Bunza a jihar.
Wadanda ake zargin sun hada da Sanusi Muhammad da Ibrahim Lawal daga Jihar Sokoto da Tasi’u Abubakar da Tasi’u Abdullahi daga Jihar Zamfara, an kama su ne bayan da jami’in ‘yansanda reshen Bunza da tawagar ‘yan banga suka kai daukin gaggawa.
- Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
- Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)
Kakakin rundunar ‘yansandan, CSP Nafiu Abubakar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce wadanda ake zargin sun cika harabar makarantar ne da misalin karfe 3 na dare, inda suka daure mai gadin makarantar kafin daga bisani suka fasa na’urar taranfoma dake daure da sarkoki da sauran kayan aikin injiniya.
Ya ce, “An gano wata bakar mota kirar Toyota Corolla mai lamba KNT-359-SN, wacce ake kyautata zaton wadanda ake zargin sun yi amfani da ita, a wajen da lamarin ya faru, tare da barnata wayoyi masu sulke da kuma kayan aikin da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.
“Yayin da aka kama biyu daga cikin wadanda ake zargin nan take, wani bincike mai zurfi da hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID) ta gudanar a Birnin Kebbi, ya kai ga kama ‘yan kungiyar da suka gudu.”
Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna nan a gidan yari kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunci.
Kwamishinan ’Yansandan Jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa kwazon da DPO da ’yan banga suka yi da gaggawa, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan ‘yansanda da al’umma wajen magance miyagun laifuka.
Ya kuma tabbatar wa mazauna Jihar Kebbi cewa, rundunar ‘yansandan ta jajirce wajen kawar da masu aikata laifuka da samar da yanayi mai tsaro. Daga nan sai ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi ta kama wasu mutane shida da ake zargi da satar kayan ado na zinare da suka kai sama da Naira miliyan 109.5 a garin Ka’oje da ke Karamar Hukumar Bagudo.
Al’amarin ya dauki hankula sosai bayan kama Ibrahim Abubakar, jami’in hukumar gidan gyaran hali ta Nijeriya, wanda ya amsa laifinsa. Kayayyakin da aka sace na iyalan Hajiya Amina Hassan Bello, sun hada da sarkar gwal guda biyar, bangulu guda tara, da zobe hudu masu nauyin gram 782.7.
A cewar rundunar ‘yansandan, dansandan ya hada baki ne da ‘yan fashin wajen sayar da gwal din da aka sace tare da karkatar da kudaden ta hanyar mallakar filaye. Ana ci gaba da gudanar da bincike don zakulo wasu da ake zargi da kuma kwato wasu kadarori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp