Sashin masu aiki da kafin basira (IRT) na hukumar ‘yansandan Nijeriya, ta samu nasarar cafke wasu masu suna Okechukwu Edison da Sunday Morison bisa zarginsu da yin garkuwa da fashi da makami ga wata Lauya a Fatakwal da ke jihar Ribas. Â
Binciken farko-farko ya nuna wadanda Ake zargin duk sun fito ne daga kauyen Rumuji da ke karamar hukumar Emohua a jihar Ribas, sun jima kuma sun kware wajen garkuwa da mutane, fashi da makami, kwacen motoci wadanda suka tsere daga gidan yari a Imo.
Bayan da suka samu nasarar shirya garkuwa da wata Lauya a Fatakwal, dubun wadanda ake zargin ta cika a ranar 10 ga watan Nuwamban 2022 inda aka yi ram da su a kwanar Rumuola da ke jihar Ribas.
Wadanda ake zargin biyu tare da wani abokin cin burminsu da suka aiwatar da garkuwar, sun tana shafe shekaru 11 a gidan gyara halinka (NCoS) a jihar Imo a matsayin masu jiran hukunci kan zargin aikata garkuwa da mutane.
Wadanda ake zargin sun amsa laifukansu ga IRT da DCP Tunji Disu ke jagoranta da cewa, “mun bar gidan yari a ranar Litinin 5 ga watan Afrilun 2022 a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki gidan yarin Kuma suka umarci fursunoni da su gudu.
“Mun shiga harkar garkuwa da mutane, fashi da makami gami da kwacen motoci ne bayan da wasu sojoji suka mamayi tare da lalata wurin da muke harkar Mai bayan samun ‘yanci daga tserewar gidan yari don mun rasa komai da za mu yi rayuwa da cigaba da kula da iyalanmu.”
Dubun masu garkuwan ta cika ne bayan da jami’an IRT suka samu bayanin yin garkuwar da lauyar da suka boyeta na tsawon kwanaki uku.
Lauyar ta samu tsira bayan da aka cafke wadanda ake zargi da yin garkuwa da iya kuma sun sace mata kudi naira miliyan 5 a asusun ajiyarta.