Wani matashi dan shekara 26, Franklin Akinyosuyi, wanda aka kama shi da sassan jikin mutum a garin Ondo, hedikwatar karamar hukumar Ondo ta Yamma a jihar Ondo, ya ce ya yi wanka da kan mutum tsawon wata guda domin bunkasa kasuwancinsa.
Akinyosuyi, wanda ake zargin dan damfara ne kuma dan tsibbu, jami’an sashin yaki da laifuffuka da ke ofishin ‘yansanda na Funmbi-Fagun, a cikin garin Ondo ne suka cafke shi.
Wanda ake zargin ya ce ya yanke shawarar zuwa wajen Boka ne sabida matsananciyar wahalar rayuwa da ke barazana ga kasuwancinsa.
Ya bayyana hakan ne yayin da ake gabatar da shi tare da wasu mutane biyar a hedikwatar rundunar da ke Akure, babban birnin jihar Ondo. Ya kuma amsa cewa, an ga kan Mutum a gidansa da yake haya da ke unguwar Elewuro.