Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina, ta dakile yunkurin sace mutane a kan hanyar Magama zuwa Jibia.Â
Yan bindiga sun kai wa motocin haya guda biyu hari, inda suka yi kokarin sace fasinjoji.
- An Fitar Da Tsarin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa A Fannin Raya Masana’Antu Da Rarraba Hajoji Na Beijing
- An Gano Buhunan Shinkafar Tallafi 16,800 Mai Nauyin Kilo 50 Da Aka Sauyawa Buhu A Kano
Sai dai jami’an ‘yansanda daga Jibia sun isa wajen da a kan lokaci, inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar, wanda hakan ya sa suka tsere.
‘Yansanda sun samu nasarar ceto mutum 14.
Amma, mutum biyu daga cikin wadanda aka ceto sun samu raunin harbin bindiga.
An garzaya da su asibiti don ba su kulawa, kuma rahotanni sun nuna cewa suna cikin koshin lafiya.
Kakakin Rundunar ‘Yansanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya yaba wa jami’an da suka nuna jaruntaka tare da daukar matakin gaggawa.
Ya tabbatarwa da al’umma cewa ‘yansanda za su ci gaba da aiki tukuru don yaki da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaro.
Adejobi, ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su hada kai da jami’an tsaro ta hanyar ba su bayanai kan duk wani motsi ko aikata laifi.
Ya ce hadin kan al’umma yana da matukar muhimmanci wajen yaki da ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka.