Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ta ce ta ceto wasu mata 9 da ake zargin yi safararsu.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Gambo Isah a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce an ceto mutanen ne bisa sahihan bayanan sirri, inda ya ce jami’an tsaro sun kai samame wata maboyar Daura tare da kubutar da mutane tara da aka kashe.
- OPEC Ta Rage Adadin Man Da Nijeriya Za Ta Rika Fitarwa Kasuwannin Duniya
- Mutum 30 Sun Nutse A Ruwa Yayin Tsere Wa Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Ya lissafa wadanda aka ceto kamar haka; Safiyyat Ahmed (21) daga Jihar Legas, Precious Nuhu (22) daga Jihar Kaduna, Bolanle Adewusi (32) daga Ogun, Okpoekwu Eunice (28) daga Jihar Enugu, Kabirat Azeez (19) daga Jihar Ondo da Taiwo Adeolo mai shekaru 27, daga jihar Ondo.
Sauran wadanda aka ceto sun hada da, Timilaye Ojo mai shekaru 26 daga Jihar Legas, Blessing Joseph mai shekaru 19 daga Edo, sai kuma wata Khadija Abdullahi mai shekaru 29 daga Jihar Ondo.
Ya ce a yayin gudanar da bincike, wadanda abin ya shafa sun bayyana cewa wani direba ne ya dauke su daga Jihar Kano zuwa Daura, wanda a lokacin da suka ga tawagar ‘yansandan ya watsar da wadanda lamarin ya rutsa da su.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don tabbatar da ko akwai wasu a cikin gidajen da jihar ta shafa.
Wadanda abin ya shafa sun ce suna kan hanyarsu ta zuwa kasar Libiya ta Jamhuriyar Nijar ne aka ceto su, kamar yadda Isah ya sanar.