Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta ceto mutane uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai harin a Arab Road Extension 2 da ke gundumar Kubwa a Abuja da yammacin ranar Talata.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma tabbatar da cewa ‘yan bindigar a yayin harin sun harbe mutum biyu, wani mashahurin tela a yankin mai suna Oshodi wanda ya mutu nan take, sai wani kuma da yanzu haka yake jinya a wani asibiti.
Kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, DSP Josephine Adeh, wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce: “Bincike na farko ya nuna cewa da misalin karfe 7:30 na yamma na ranar 6 ga watan Disamba, 2022, wasu ‘yan fashi da makami sun afka wasu jerin gidaje da ke Kubwa, inda suka harbe mutum biyu, Oshodi da wani Abdulwahab.
Ta ci gaba da cewa, ‘yan sandan sun fara gudanar da bincike kan lamarin duk da cewa an kai ga farautar wadanda suka aikata wannan aika-aika, inda aka yi nasarar ceto mutane uku daga cikin wadanda aka sace tare da kwato bindiga kirar AK47 daya da alburusai 25.