Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara sun samu nasarar kubutar da mutane tara da ‘yan bindiga suka sace a ranar Talatar da ta wuce a kauyen Kucheri da ke a cikin karamar hukumar Tsafe ta jihar.
Wadanda aka kubutar sun hada da mata bakwai da maza biyu.
- Yadda Furucin Dakta Idris Kan Manzon Allah Ya Janyo Zafafan Muhawara A Bauchi
- Fyade: Abubuwan Da Ke Hadasawa, Illoli Da Yadda Za A Magance
A cewar kakakin rundunar ‘yansandan jihar, CSP Mohammed Shehu Anipr, jami’an sun samu nasarar kubutar da mutanen ne, bayan samun bayanan sirri daga wajen wani mutum, inda jami’an suka yi amfani da bayanan suka kubutar da mutanen a cikin koshin lafiya.
Shehu ya bayyana cewa, wadanda aka kubutar an duba tafiyarsu a Gusau, daga bisani aka mika su ga ‘yan uwansu.
Kwamishinan rundunar ‘yansandan jihar, Kolo Yusuf ya jinjina wa kokarin jami’an kan kubutar da mutanen, inda ya bai wa al’ummar jihar tabbacin ci gaba da yakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.