Rundunar ‘yansandan Jihar Filato, ta ce jami’anta sun cafke wadanda suka yi garkuwa da Sarkin kabilar Izere a karamar hukumar Jos ta Gabas, Dakta Azi Wakili.
A wata sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, DSP Alfred Alabo ya fitar, ya ce bayan samun kiran wayar gaggawa da suka yi daga caji ofis din Angware da ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kutsa kai gidan Agwom Izere, Dakta Azi Wakili tare da yin garkuwa da shi.
- Yadda Za Ka Sauke Bidiyo A Wayarka Daga Facebook Da YouTube
- Da Dumi-duminsa: An Sace Basarake Mai Daraja Ta Ɗaya A Jihar Filato
Sanarwar ta ce, nan da nan rundunar ‘yansandan karkashin jagorancin DPO na Angware, SP Timothy Bebissa, suka isa wajen cikin gaggawa a yayin da jami’ansu guda ya gamu da rauni yayin da wani farar hula (Dan tsaron sa-kai) ya mutu sakamakon harbin da ‘yan bindigar suka masa.
Ya kara da cewa bisa kokarin ‘yansandan da hadin guiwar jami’an tsaro sa-kai na ‘yan banga sun ceto Sarkin daga hannun wadanda suka sace shi.
Ya kara da cewa wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin sun shiga hannu.
Kakakin ya kara da cewa, dan sandansu da aka raunata yanzu haka yana asibiti yayin da kuma gawar wanda aka kashe aka kai ta dakin ajiye gawarwaki.
Ya tabbatar da cewa tuni suka kaddamar da bincike kan lamarin tare da shan alwashin za su kamo maharan da suka aikata laifin.