• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Abuja

by Naziru Adam Ibrahim
1 year ago
Abuja

Jami’an Rundunar ‘Yansanda ta birnin tarayya, Abuja, karkashin jagorancin kwamishina CP Benneth Igweh, sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a unguwar Dawaki da ke Abuja ranar Lahadi.

Kakakin rundunar ‘Yansandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, cikin gaggawa da dabaru na mayar da martani ga harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai a garin Dawaki a ranar 19 ga Mayun shekarar 2024, da misalin karfe 11:30 na dare, jami’an rundunar karkashin jagorancin Kwamishinan CP Igweh, da kansa sun yi gaggawar zuwa inda lamarin ya faru.

  • Yaushe Za A Dakatar Da Yi Wa `Yan Arewa Kisan Gilla?
  • Mi’ara Koma Baya: CBN Ya Janye Dokar Cazar Kaso 0.05 A Banki

Cikin jarumtaka da hadin kai, ‘yansanda tare da hadin gwiwa da mafarauta, suka ci gaba da kai farmaki kan maharan, inda suka yi musu kwanton bauna a tsaunin Ushafa na Bwari da tsaunin Shiship na Mpape tare da musayar wuta wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa da raunuka daban-daban inda ‘Yansandan suka yi nasarar ceto jama’ar.

Daya daga cikin wadanda aka ceto na kwance a asibiti ana kula da lafiyarsa inda kwamishinan ‘Yansandan ya jaddada jajircewar rundunar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda aka yi garkuwa da su da suka tsere daga wurin yayin musayar wuta.

Yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 12 da suka hada da mata 8 da maza 4 a unguwar Frank Opara Street da ke Dawaki a Abuja.

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
Manyan Labarai

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
Manyan Labarai

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Next Post
Wang Yi: A Tsaya Kan Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin Mashigin Teku Na Taiwan

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.