Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa.
Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan titin garin Mubi a ɗimauce.
Anan ne, jami’an ‘yansandan suka ceto yaran da suka hada da Adamu Musa, Suleiman Idris, Suleiman Mohammed, Dauda Yahaya da Mohammed Alhassan, dukkansu mazauna garin Gwange, Maiduguri, jihar Borno.
Binciken da ‘yansanda suka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa wani mai suna Aliga Suleiman na Sabon Layi, Gwange, Maiduguri ne ya ɗauko yaran daga Maiduguri ba bisa ƙa’ida ba.
‘Yansandan sun ce ana ci gaba da kokarin cafke wanda ake zargin tare da gurfanar da shi gaban kotu.
Kwamishinan ‘yansanda na rundunar, CP Dankombo Morris ya yabawa kwamandan yankin da tawagarsa bisa nasarar ceto yaran, ya kuma umurci sashen binciken manyan laifuka na jihar da ya ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp