Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq, ya ce rundunar ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da ƙwato bindiga kirar AK-47 daya da babur daya a ranar Juma’a.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Litinin a Katsina.
“Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta yi nasarar dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane, inda ta ceto wani da aka yi garkuwa da shi, sannan ta kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, sannan ta kwato babur guda daya a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
“A ranar 2 ga Mayu, 2025, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da makamai sun kai hari kan wani Abu Iro, wani matashi dan shekara 23 a karamar hukumar Faskari, inda suka Sara masa Adda a kokarinsu na tafiya da shi.
“Bayan samun rahoton, cikin gaggawa tawagar jami’an ‘yansanda tare da kungiyar tsaro ta cikin al’umma ta jihar Katsina (KSCWC), karkashin jagorancin babban jami’in tsaro na Faskari, suka amsa kira, inda suka dakile yunkurin yin garkuwa da mutane, tare da samun nasarar kubutar da wanda aka sace.” In ji Sadiq
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp