Rundunar ‘Yansandan jihar Zamfara ta yi nasarar dakile wani shirin ‘yan bindiga na kai hari Masallacin Juma’a a kauyen Kwata da ke karamar hukumar Zurmi.
Kakakin rundunar, ASP Yazid Abubakar ne, ya bayyyana haka a taron manema labarai a Gusau.
- Gwamnatin APC Ta Kara Ingiza ‘Yan NIjeriya Cikin Bakin Talauci – PDP
- Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Kokarin Magance Tushen Matsalar Karancin Abinci
Yazid ya bayyyana cewa, jami’an sun samu rahoton sirri kan shirin kai harin wanda nan take suka dauki matakin dakile harin.
Ya kara da cewa, maharan sun kai kimanin mutane biyar dauke da makamai a kan babura wanda ake zargin ‘yan bindiga ne da ke shirin kai hari lokacin sallar Juma’a a kauyen Kwata da ke Karamar hukumar Zurmi.
“Anan take jami’anmu sukai artabu da ‘yan bindigar wanda ya dauki tsawon sa’a guda ana yi, inda aka kashe daya daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka tsere zuwa daji suka bar bindiga AK47 guda biyu, alburusai da kuma babur kirar Bajaj.”
Haka zalika, jami’an da ke aiki a Zurmi sun samu rahoton sirri cewa wasu gungun ‘yan bindiga na shirin kai hari kan jami’an ‘yansanda a karamar hukumar Zurmi.
A cewar kakakin da samun labarin, DPO ya jagoranci tawagar da suka binciki lamarin wanda ya yi sanadin cafke wata mata ‘yar shekara 35 mai suna Umma Zubairu da ke kauyen Rukudawa da ke Awala ta hanyar Nasarawan Zurmi.
“Lokacin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa, tana aiki da dan fashi mai suna ‘Dan karami Gwaska’ a matsayin mai ba shi bayanai kuma an tura ta ne ta sanya ido kan ‘yansanda a Zurmi domin su kai hari.”