Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta kaddamar da bincike kan rasuwar kwatsam da ta afkawa wani mai yi wa kasa hidima (NYSC) a karamar hukumar Dambam.
Marigayin, mai suna Nwokedi Chukwuebuka mai shekaru 28, an same shi ba rai a masaukinsa da sanyin safiyar Lahadi, 10 ga Agusta, 2025.
- Gwamnatin Kano Za Ta Horar Da Tubabbun ‘Yandaba 718 Sana’o’i
- Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa
A cewar ‘yansanda, an tanadi masaukin ne ga masu yi wa kasa hidima (NYSC) da jami’in da ke kula da su (CLO).
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi.
“CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil.
Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin.
An garzaya da Chukwuebuka zuwa wani asibiti da ke kusa, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Daga bisani, aka akai gawarsa zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare, kamar yadda doka ta tanada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp