An samu karin bayani game da kisan gilla da wasu matasa suka yi wa wata yarinya a Jihar Neja bisa zargin yin kalaman batanci ga Addinin Musulunci.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, wacce ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta ce an kone yarinyar, wacce aka fi sani da suna Ammaye, kafin isowar jami’an tsaro domin kawo dauki.
Mai magana da yawun rundunar, Wasiu Abiodun, wanda ya fitar da sanarwa kan lamarin, ya ce ana ci gaba da kokarin gano, kamawa da gurfanar da duk wadanda ke da hannu wajen wannan aika-aika.
Ammaye, wacce ke sana’ar sayar da abinci, matasa ne suka kashe ta suka kuma kone a Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja bisa zargin Batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Bisa ga bayanan ganau, lamarin ya faru ne a Kasuwar Garba a yankin karamar hukumar, lokacin da Ammaye, wacce Musulma ce kuma sananniyar mai sayar da abinci, ta yi muhawara da wani saurayi da ake cewa dan uwanta ne.
An ce saurayin ya yi wa Ammaye wasa da cewa yana son aurenta domin “cika Sunnah”. Sai dai kuma an ce Ammaye ta yi wata magana da aka dauka a matsayin Batanci.
Wannan ne ya fusata matasan yankin. Lamarin aka kai shi fadar Dagacin Kasuwar Garba, inda aka yi mata tambayoyi, kuma a cewar rahoto ta maimaita abin da ta fada tun farko.
An ce Dagacin ya mika Ammaye ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike, amma taron matasa masu hargitsi suka mamaye jami’an tsaro, suna cewa a kashe ta nan take.
Jaridar PUNCH Metro ta gano cewa kafin jami’an tsaro su iso domin kawo dauki, matasan sun riga ya jajjefe Ammaye har ta mutu.
Mai magana da yawun ‘yansandan Jihar Neja ya bayyana cewa wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Asabar, misalin karfe 2:00 na rana.
A cewarsa, “An samu rahoton cewa wata mace mai suna Amaye, mazauniyar Kasuwan-Garba a Karamar Hukumar Mariga, ta yi wasu kalamai da aka dauka a matsayin masu saba wa da Addinin Musulunci. Wannan magana ta tayar da hankalin jama’ar yankin.
“Abin takaici, hakan ya janyo taron matasa suka kai mata hari, suka kone ta kafin isowar jami’an tsaro da aka tura domin kai dauki,” in ji Abiodun.
Abiodun ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar doka a hannunsu, su kuma bar jami’an tsaro su gudanar da aikinsu bisa tanadin doka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp