• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Hallaka Ɗan Fashi Da Makami Tare Da Jikkata Wasu Da Dama A Bauchi 

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
3 months ago
in Labarai
0
‘Yansanda Sun Hallaka Ɗan Fashi Da Makami Tare Da Jikkata Wasu Da Dama A Bauchi 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Bauchi sun kashe wani da ake zargin ɗan fashi da makami ne mai suna Abdu Shagari ɗan shekara 24 a duniya, a yayin wata arangama da suka yi da ‘yan fashin a kan babban hanyar Toro zuwa Jos. 

Kazalika, wasu daga cikin ‘yan fashin sun samu damar tserewa da harbin bindiga da sauran raunuka daban-daban a jikinsu zuwa dazuka.

  • Sabbin Matakan Amurka Game Da Masu Shiga Kasar Sun Ci Karo Da Ikirarinta Na Mutunta Hakkokin Bil Adama
  • Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Ta’adda, Sun Kashe Wasu Da Yawa A Borno

CSP Ahmed Mohammed Wakil, jami’in watsa labarai ne a shalkwatar hukumar ‘yansandan ta jihar Bauchi, ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Alhamis.

Labarai Masu Nasaba

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025.

Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro, tare da haɗin guiwar sauran jami’an tsaro inda suka nufi wurin da nufin daƙile fashin.

Da isarsu wurin, suka fara musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu wanda hakan ya janyo da dama daga cikin ‘yan fashin suka gamu da raunuka na harbin bindiga sannan an harbe daya ya mutu nan take.

LEADERSHIP ta rawaito cewa, an miƙa gawar Shagari ga sashin da ke kula da gawarwaki domin birne shi kamar yadda aka tanada.

Wakil ya ƙara da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin ganin an bi sawun sauran waɗanda ake zargin ‘yan fashi da makamin ne da suka tsere domin tabbatar da an kamo su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Lambar “-1.5” Gargadi Ce Da Al’ummar Duniya Ke Yi Ga Azzaluma 

Next Post

Ma’aikatar Harkokin Waje: Kasar Sin Ta Kasance Gwarzuwa Wajen Samar Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

Related

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?
Labarai

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

14 minutes ago
Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya
Kotu Da Ɗansanda

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

1 hour ago
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe

2 hours ago
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano
Manyan Labarai

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

3 hours ago
Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji
Kotu Da Ɗansanda

Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

4 hours ago
Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara
Tsaro

Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

5 hours ago
Next Post
Ma’aikatar Harkokin Waje: Kasar Sin Ta Kasance Gwarzuwa Wajen Samar Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

Ma’aikatar Harkokin Waje: Kasar Sin Ta Kasance Gwarzuwa Wajen Samar Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

LABARAI MASU NASABA

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

August 23, 2025
Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

August 23, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe

August 23, 2025
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

August 23, 2025
Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

August 23, 2025
Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

August 23, 2025
Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

August 23, 2025
Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Da Su Guji Tallata ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kama Waɗanda Suka Kashe Masallata A Malumfashi 

August 23, 2025
Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

August 23, 2025
Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.