Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta sanar da cewa, ta haramta duk wani nau’i na bukukuwa da gangami ga magoya bayan jam’iyyun siyasa kan samun nasara a zaben da aka kammala na shugaban kasa da ‘yan majalisu da wadanda ke tafe na gwamna da ‘yan majalisu a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata katardar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, (PPRO) SP Nafi’u Abubakar ya rabawa manema labarai a garin Birnin Kebbi, a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji Kontagora.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, duk wani yunkuri na karya doka ga kowace Jam’iyya ta kowace hanya, ba za a amince da ita ba, domin an baza jami’an tsaro tare da ba da umarnin tabbatar da cikakken tsaro a fadin jihar.
Ya kuma jaddada cewa, ana kira ga jama’a da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar da ake samu a jihar, domin rundunar ‘yansandan jihar tare da hadin guiwar hukumomin tsaro da abin ya shafa a jihar, sun shirya tsaf domin tunkarar masu wa doka karan tsaye kamar yadda a ka yi tanadi a dokokin kasar
Hakazalika, Kwamishinan ya tabbatar wa jama’a a fadin jihar cewa, rundunar ‘yansandan jihar za ta ci gaba da jajircewa kan aikin tabbatar da tsaron jama’a da dukiyoyinsu domin ba su damar gudanar da sana’o’insu na halal ba tare da wata fargaba ko tsangwama ba.