Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina ta dakile harin wasu ‘yan bindiga tare da kashe wasu mutum biyu da suka yi kaurin suna a jihar.
Rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a Katsina.
- Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Tsallake Rijiya Da Baya Kan Shirin Tsige Shi
- An Kafa Dokar Hana Shan Sigari A New Zealand
“Kasurguman ‘yan bindigar biyu masu suna Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari an ga bayansu,” cewar kakakin ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah.
Ya kara da cewar an kashe ‘yan bindigar ne lokacin da suka kai hari yankin Sakkwato Rima da ke Karamar Hukumar Dutsinma a jihar.
“A ranar 13 ga watan Disamba 2022 da misalin karfe 7:30 ja dare, mun samu kiran agani cewar ‘yan bindiga dauke da bindigu kirar AK-47 sun kai hari yankin Sakkwato Rima a Karamar Hukumar Dutsinma da nufin sace mazauna yankin.
“Shugaban dakarun ‘yansandan yankin da tawagarsa sun kai dauki yankin, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar har suka nasarar kashe ‘yan bindigar da aka dade ana nema ruwa a jallo,” cewar Isah.
Ya kara da cewar an samo bindiga kirar AK-47 guda biyu da makamai masu yawa.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike a yankin da kewayensa don cafke karin ‘yan bindigar da suka tsere da raunin harbin bindiga.”