‘Yansanda a Jihar Delta sun kama wani da ake zargin ɗan bindiga ne mai suna Sanusi Abdulahi.
A lokacin da suka kama shi, yana ɗauke da kuɗin Naira miliyan biyar, wanda kuɗin fansa ne da aka biya domin sakin ɗaya daga cikin mutanen da aka sace.
- EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari
- VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano
Kakakin rundunar, Bright Edafe, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar Edafe, an kama Abdulahi ne a safiyar ranar 12 ga watan Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
‘Yan sanda sun kuma kama wasu mutum huɗu da ake zargi suna cikin tawagar Abdulahi.
Bincike ya nuna cewa su ne ke da hannu a wasu sace-sacen mutane a wurare kamar Ibusa, Ogwashi-Ukwu, Obulu-Okiti, Isele-Ukwu, Isele-Asagba, da kuma sace wata yarinya da ya fa Ogwashi-Ukwu a ranar 9 ga watan Yuli, 2025.
Abdulahi ya jagoranci ‘yansanda zuwa maɓoyarsu a unguwannin Second Deputy da Oko dake Asaba, inda aka kama sauran abokan aikinsa huɗu.
Edafe ya ce har yanzu bincike na gudana.