’Yansanda a Jihar Enugu sun kama wani matashi mai shekara, mai suna Chinecherem Ugwuagu, wanda ya sanya kayan NYSC domin yin basaja wajen aikata fashi da makami.
Kakakin ’yansanda na jihar, SP Daniel Ndukwe, ya ce an kama shi a kan hanyar Enugu zuws Onitsha tare da wani babur da ya sato, kaya, katin ATM, da kuma bindigar bogi da ska haɗa da kwali.
- Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka
- Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu
Bincike ya nuna cewa Ugwuagu ya shiga gidan wani mutum a 9th Mile, cikin Karamar Hukumar Udi, inda ya tsoratar da shi da bindigar ƙarya sannan ya sace abubuwan da aka samu a wurinsa kafin ya yi ƙoƙarin tserewa cikin kayan NYSC.
’Yan sandan da ke sintiri a hanya suka lura da shi suka kama shi. Za a gurfanar da shi a kotu bayan an kammala bincike.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Enugu, CP Mamman Bitrus Giwa, ya yabawa jami’an da suka yi aikin da sauri, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai don taimakawa wajen tabbatar da tsaro a jihar.