Rundunar ‘yansandan Jihar Taraba ta kama wani da ake zargin dan bindiga ne tare da kin karbar cin hancin Naira miliyan 8.5 daga hannun mutumin.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Taraba, CP Joseph Eribo ne, ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wasu da ake zargi da aikata laifuka a jihar.
- Sin: Taimakawa Lardin Hunan Don Habaka Hadin Gwiwa Da Afirka
- Bahar: Nasarorin Da Sin Ta Cimma A Fannin Makamashi Mai Tsafta Abin Misali Ne Ga Daukacin Duniya
Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin karfe 9:45 na dare a cikin wata mota kirar Toyota Starlet mai lamba YLA 321 ZY a kan titin Jalingo zuwa Yola.
“Ya gaza bayar da bayani game da kansa a lokacin da ake masa tambayoyi, saboda haka binciken motarsa ya sa aka gano abubuwa kamar haka: miliyan takwas da dubu dari biyar da hamsin da biyar (N8,555,000), wayoyi, layin MTN da sauran kayayyakin zargi,” in ji Eribo.
“Wanda ake zargin ya yi yunkurin bai wa jami’an PMF cin hanci, inda ya ba su dukkanin kudaden da ke tare da shi domin su sake shi, amma jami’an suka ki amincewa”
A wani labarin kuma, dakarun bataliya ta 144 da ke Jalingo sun yi artabu da ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu mutane uku a babban birnin jihar.
Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, Laftanar Olubodunde Oni, ya bayyana cewa arangamar ta faru ne a lokacin da ‘yan bindigar ke kan hanyar zuwa Yorro.
Ya tabbatar da cewa an ceto mutanen da aka sace sannan an sada su da iyalansu.