Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, ta ƙwato wayoyi 126 da aka sace daga masu laifi 26 da ta kama waɗanda ake zargi da satar wayoyin a jihar.
Kakakin rundunar, SP Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan, inda ya ce sun samu nasarar kai wani samame da suka gudanar tsakanin ranar 1 zuwa 12 ga watan Satumban 2024, a wani mataki na magance masu ƙwacen waya da fashi da makami a jihar.
- Abubuwan Da Ake Sa Ran APC Ta Tattauna A Taron Kwamitin Zartarwarta
- Ambaliya: Uwargidan Gwamnan Yobe Ta Janjanta Wa Al’ummar MaiduguriÂ
A cewarsa, wannan mataki ya biyo bayan umarnin babban sufeton ‘yansandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ga ‘yansanda da su kai sumame wuraren da ɓata-gari ke amfani da su wajen aikata laifuka.
Sauran abubuwan da suka ƙwato daga wadanda ake zargin, sun haɗa da alluran maye 21 da ƙwayar diazepam guda 600 da exol fakiti uku da sauran busassun ganye masu yawa da ake zargin tabar Wiwi ce da almakashi biyu da takobi daya da kwamfyuta guda biyu.
Kiyawa, ya kuma kara da cewa, wayoyin da aka Æ™wato za a mayar da su ga masu su da zarar sun kammala tantance su wanda ya ce tuni sun fara gudanar da aikin hakan ta hanyar amfani da na’urar mai Æ™waÆ™walwa.
Da yake neman haɗin kai da goyon bayan jama’a don daƙile duk wani nau’in aikata miyagun laifuka a jihar, kakakin ya ce a halin yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin.
Ya ce da zarar sun kammala binciken za a gurfanar da su a gaban kotu don su girbi abin da suka shuka.