Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce, ta kama wasu mutane 58 da ake zargi da hannu a fashi da makami da garkuwa da mutane a jihar.
Da yake baje kolin wadanda ake zargin, kwamishinan ‘yansandan jihar, Dankombo Morris ya ce, wadanda aka kama sun hada da ‘yan fashi da makami guda bbakwaida masu garkuwa da mutane 11 da ake zargi.
- Gwamnatin Zamfara Za Ta Zamanantar Da Asibitin Kwararru Na Yeriman Bakura Da Daga Darajarsa
- Dole Ne A Hukunta Wadanda Suka Kashe Sojoji A Delta – Tinubu
CP Morris ya ce, an kama su ne a cikin makonni hudu da hawansa kan sabuwar kujerarsa.
Morris ya ce, daga cikin wadanda ake zargin, akwai 40 daga cikin wadanda ake kira da ‘ya’yan Shila – kungiyar wasu matasa ne da ke addabar mazauna jihar.
Ya ce, an kama yaran ‘yan’yan Shila ne a wani wurin da ake kira dajin Sambisa, inda suka yi imanin cewa, wurin shi ne babbar mafaka ga masu aikata manya-manyan laifuka a jihar.
CP ya kara da cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.