Rundunar ‘yansandan jihar Neja ta kama wasu mutane biyu bisa laifin yin garkuwa da wani yaro dan shekara 10 da haihuwa a karamar hukumar Mariga.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, da ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa, an yi garkuwa da yaron ne mai suna Yaseer Mustapha mai shekaru 10 da haihuwa, mazaunin Kwanar-Mariga a ranar 24 ga Yuli, 2025.
- An Fara Nuna Hotuna Da Shirye-Shiryen Bidiyo Da Matasan Kasa Da Kasa Suka Dauka Don Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafa MDD A Kasar Sin
- Wa’adin Mulki Ɗaya Kacal Za Ka Yi — ADC Ga Tinubu
Mai kula da Yaseer ne ya samu kiran gaggawa lokacin yana kan aikin gona cewa, ana neman kuɗin fansa naira miliyan 3.5
“Bayan tattaunawa mai yawa, aka samu damar tara ₦100,000, wanda ya biya a cikin asusun da masu garkuwa da mutanen suka bayar, bayan wata ɗaya, sai aka bukaci ya biya wani Abdulmajid Dan-Azumi karin ₦10,000, ba tare da sun saki yaron ba,” Abiodun ya bayyana.
Waliyyin da ya fahimci lamarin ba mai ƙarewa ba ne, sai ya kai rahoto ga ‘yansanda a watan Satumba, inda nan take aka mayar da karar zuwa sashin yaki da garkuwa da mutane na SCID.
‘Yansandan sun bi sawun Abdulmajid Dan-Azumi mai shekaru 32 dan garin Kwana, wanda, daga nan aka yi nasarar kama abokin hulɗarsa, Abdulnafiu Usman wanda suke zaune duk a unguwa ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp