Rundunar ‘Yansanda a Sabon-Gari a Zariya, Jihar Kaduna, ta kama wasu ‘yan kungiyar asiri 13 da kuma masu fashi da makami.
Mukaddashin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ne ya bayyana a ranar Litinin a Zariya.
- ZARGIN MAITA: Mahaukaciya Ta Razana Al’umma A Kaduna
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 Tare Da Cafke 9 A Jihar Kaduna.
‘Yan kungiyar sun riga sun amsa cewa su ‘yan kungiyar “Eiye’’ Confraternity ne.
“Sun fito ne daga manyan makarantu daban-daban a fadin kasar nan kuma suka zabi wani bangare na Zaria a matsayin wurin baje-kolinsu,” in ji shi.
Hassan ya bayyana cewa, ‘yan kungiyar asiri sun kai farmaki kan al’ummar Zaria a ranar Lahadin da ta gabata dauke da adduna da sauran muggan makamai.
Ya kara da cewa sun shiga gidaje sun jikkata tare da yi wa mutanen fashi kafin su gudu zuwa wani dajin da ke kusa.
Kakakin ya bayyana cewa, jami’an ‘yan sanda sun bi sawun maharan zuwa maboyar su da ke cikin dajin tare da cafke 13 daga cikinsu yayin da wasu kuma suka kara gudu.
Hassan ya kara da cewa wadanda aka kama suna ba ‘yan sanda hadin kai a kokarin da suke na cafke wasu ‘yan kungiyar.