Rundunar ‘yansanda da ke Saminaka a Jihar Kaduna, ta cafke wani matashi mai suna Abdulkarim Usman Maude mai shekaru 33 daga Tudun Wada Mariri a Upara Warsapiti a karamar hukumar Lere a jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Mansir Hassan ya fitar, ya ce, an kama wanda ake zargin ne dauke da jaka da kudi kimanin Naira 347,000 aciki tare wuka da kayan tsafi.
- Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Rabon Kayayyakin Amfanin Gona Ga Manoman Kaduna 40,000
- Mozambique: An Shirya Maido Da Noman Alkama Bisa Tallafin Fasahohin Kasar Sin
Yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin garkuwa da mutane a karkashin dabar wani Alhaji Yakubu inda suka yi garkuwa da wasu mutane biyu daga kauyen Binchim da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
Kakakin rundunar ‘yansandan ya ci gaba da cewa, kudaden da aka kwato, wanda ake zargin ya ce, kasonsa ne da aka bashi bayan sun yi garkuwa da wasu ma’aikatan taraktoci biyu, Ya’u Balele (mai shekaru 45) da Lukman Abubakar (mai shekaru 40) da aka sace a ranar 17 ga Mayu, 2024, yayin da suke kan aiki a gonar wani Alhaji Gambo.