Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wani da ake zargin barawon mota ne tare da kwato wata mota da ya sace.
Rundunar a cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Litinin ta bayyana cewa, sashin rundunar mai yaki da satar motoci ya gano wata mota kirar Toyota Rav-4 da aka yi watsi da ita mai lamba YAB 881 JK, Abuja, yayin wani bincike a Kwanar Ungogo, a karamar hukumar Ungogo, ranar 28 ga Disamba, 2024.
- Shekaru 62 Na Gwamnan Kano Sun Yi Albarka – Auwal Lawal
- Ba A Kowane Irin Matsayi Zan Iya Fitowa A Cikin Shirin Fim Ba – Isa Bello Ja
Kiyawa ya ce, binciken da aka gudanar bayan gano hakan ya sa aka kama wani Bala Sani mai shekaru 40, wanda ya fito daga karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.
A cewar Kiyawa, an kama Sani ne a ranar 4 ga watan Junairu, 2025, a Kwado kwatas da ke jihar Katsina.
Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin satar motar a garin Zariya da ke jihar Kaduna.
Wanda ake zargin ya kuma amince da cewa, ya tuka motar zuwa Kano da nufin siyar da ita, amma ya bar ta a kwanar Ungogo bayan ya ga jami’an ‘yansanda.
Kiyawa ya kara da cewa, motar a halin yanzu tana hannun hukumar ‘yansandan jihar Kano, yayin da ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike.
Don haka, Rundunar na kira ga mai motar da aka sace kuma aka kwato da ya kai rahoto ga ofishin hulda da jama’a na ‘yansanda tare da shaidar mallakarsa ko kuma a tuntubi 08067885568.