Guda daga cikin dattawa a Masana’antar Kannywood, wanda ya shafe fiye da shekara 40 a masana’antar a Nijeriya; Malam Isa Bello Ja (Dattijon Arziki) ya bayyana cewa, ko kadan bai dauki wannan sana’a ta dirama ko wasan kwaikwayo da wasa ba.
Amma hakan, ba zai zama dalilin da zai sa ya yi wani abu da zai zubar masa da mutuncin da ya shafe shekara da shekaru yana nema wa kansa ba. Ya kara da cewa, duk wani abun alheri da mutum zai iya samu a sanadiyar sana’arsa; shi ma ya samu a wannan harka ta wasan kwaikwayo, kama daga zama da manyan mutane masu daraja da mutunci da kuma soyayya da kauna da ya samu daga masoya.
- Daga Karshe, Yahaya Bello Ya Fada Hannun EFCC
- Babu Wata Sana’a Da Take Da Daukaka Da Samu Irin Harkar Fim – Hajara Usman
Amma duk wannan ba zai sa ya fito a matsayin barawo ko dan daudu ko mashayin giya ko kuma mai neman mata ba, domin kuwa tun kafin ya tara iyali yake wannan harka bai yi wani abin ashsha ba; ballantana yanzu da ya tara iyali da surukai da sauran yan’uwa da abokan arziki.
“Tun kafin na shiga harkar fim, na yi aiki a wuraren gwamnati da dama da sauran sana’oi, domin kuwa duk wata sana’a a wajena sana’a ce; don Bahaushe na cewa, babu maraya sai rago, zan iya yin dukkannin wata sana’a don na rufawa kaina asiri, saboda haka, akwai bukatar na tsare mutuncina tare kuma da na sana’ata; wadda nake matukar alfahari da ita”, in ji Ja.
Tun bayan fara wannan sana’a ta dirama da na yi kawo yanzu, zan iya cewa; na yi fina-finai fiye da tunanin mai tunani, daga cikinsu akwai wadanda na fi so fiye da sauran, wadannan kuwa su ne kamar ‘Kowa Ya Bar Gida, Bakan Gizo, Hadarin Kasa da sauran makamantansu, duk wadannan fina-finan ko bayan mutuwata idan aka kalla; babu wanda zai yi tir da ni ko kuma a ce iyalina sun ji kunyar ganina a cikinsu.
Daga karshe, Bello Ja ya shawarci matasa masu shigowa masana’antar Kannywood; da su dinga tsarkake niyyarsu suna yin aiki tsakaninsu da Allah, sannan kada su yi wani abun ashsha da zai sa a yi wa masu harkar fim kudin goro wajen kiran su da mutanen banza, inda ya ce duk wanda ya jawo aka zagi ‘yan fim, bai kyauta wa mutanen arzikin da ke cikin masana’antar ba.