Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kokarin hada baki da ‘yan bindiga domin kai hare-haren ta’addanci a jihar.
Rundunar ‘Yansandan ta kuma tabbatar da cewa, ta kara tsaurara matakan tsaro a fadin jihar.
- Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru
- Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Asabar, ta ce, an kama mutanen ne a lokacin wani samame da aka gudanar da misalin karfe 2 na daren ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, a cikin garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Shanono ta jihar.
“Yayin da ake gudanar da samamen bisa ga bayanan sirri daga wasu mazauna garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Shanono, jami’an hadin gwiwa na rundunar yaki da ta’addanci ta rundunar da kuma jami’an rundunar da ke Shanono, sun gudanar da samamen na kwarewa a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 02:00 na dare. Hakan ta sa, an samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Farin Ruwa, yana mai bayyana yadda suka bayar da bayanan sirrin a matsayin muhimmin abu ga nasarar aikin. Ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani motsi ko ayyukan zargi a yankunansu.











