Rundunar ‘yansandan Jihar Neja ta kama mutum 11 bisa zargin shiga harkar ƙungiyoyin asiri da kuma satar kifin wani mutum.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an kama Idris Hamza da Suleiman Damilare a unguwar Fadikpe da tabar wiwi, kayan tsafi, da mota ƙirar Toyota Corolla a gidan wani Abdullahi Ahmed da ake kira Catch-up.
- Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
- Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
Sun amsa cewa sun ‘yan ƙungiyar asiri ta Neo Black Movement of Africa (NBM) ce, inda suka kuma bayyana cewa suna gudanar da ayyukansu a jihar har da ɗaukar sabbin mambobi a Jami’ar IBB Lapai.
Binciken ya kai ga kama wani Abdulsemiu Basir, wanda ake zargin ɗan ƙungiyar asiri ta Vikings ce mai adawa da NBM.
An kama shi a tashar mota a Lapai da layin waya guda 16, na’urar PoS, da kuɗi har Naira 77,000.
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.
A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.
Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp