Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar mafarauta sun kashe wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a Dajin-madan, da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a safiyar ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce an kashe ‘yan bindigar ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da hadin gwiwa da masu sa ido da ke cikin al’ummomin da abin ya shafa.
- Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno
- Masana Kimiyyar Sin Sun Kirkiro Sabuwar Fasahar AI Mai Hasashen Zuwan Mahaukaciyar Guguwa
Ya kara da cewa, bayan artabun, wasu daga cikin ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga zuwa dazukan da ke kusa.
Wakil ya ce, an kwato bindiga kirar AK-49 guda daya da harsashi guda tara daga hannun ‘yan ta’addan a yayin artabun.