Rundunar ‘Yansandan Jihar Neja, ta kashe masu garkuwa da mutane uku a wani samame da ta kai dajin Kokolo, Nasko a ƙaramar hukumar Magama, a ranar 12 ga watan Satumba, 2025.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda sun yi musayar wuta da masu garkuwar kafin a kashe su.
- PSG Ta Doke Barcelona Har Gida A Gasar Zakarun Turai
- Masana’antar AI Ta Kasar Sin Ta Samu Habaka Da Kamfanoni Fiye Da 5300
Sun ceto mutum ɗaya da aka sace, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
An kuma samu bindigogi ƙirar AK-74 guda biyu da harsashi 49 daga maɓoyarsu.
Abiodun ya buƙaci al’umma da su kai rahoton duk wanda suka gani da raunukan harbin bindiga.
A wani samame daban a ranar 25 ga watan Satumba, sashen Anti-Thuggery Unit ya kai farmaki maɓoyar masu laifi a Sabon-Titi, Tunga, Minna, inda aka kama wasu ɓarayi biyu.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Murtala Abbas mai shekaru 18 daga Katsina da kuma Hassan Ibrahim mai shekaru 20 daga Tunga.
An kama su da makamai irin su adduna, bindigogi ƙirar gida, rigar ‘yansanda da miyagun ƙwayoyi.
Hassan ya amsa cewa wani ɗan sa-kai mai suna “Sadiq” ne ya ba shi bindiga da kuma na’urar sadarwa wacce ba ta aiki.
Dukkaninsu suna hannun ‘yansanda a yanzu.
Haka kuma, a ranar 27 ga watan Satumba, ‘yansanda sun kama Bashir Abubakar mai shekaru 28 daga Jihar Kebbi a kasuwar Kontagora bisa zargin zamba.
An ce ya yi ƙoƙarin musanya jakar da ke cike da takardun da ba su da amfani da wayoyi da kayan haɗa da suka kai Naira dubu dari biyar (₦500,000).
An kuma danganta shi da wata zamba a watan Agusta, inda aka sace wayoyin Naira dubu 240 da kuma babur.
Mutane sun kusa yi masa dukan kawo wuƙa kafin jami’an ‘yansanda su ceci rayuwarsa.
An tabbatar da cewa za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp