Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ta kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne guda takwas tare da ceto mutane 87 da aka sace a cikin watan Mayu.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Sadiq Abubakar wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.
- Tinubu Zai Yi Sauye-sauye A Gwamnatinsa
- Nan Ba Da Jimawa Ba Majalisa Za Ta Karbi Ƙudurin Sabon Mafi Karancin Albashi – Tinubu
Ya ce an samu rahoton aikata laifuka 18 da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai, satar shanu da dai sauransu.
Abubakar, ya kuma kara da cewa an gurfanar da wasu 12 a gaban kotu, yayin da aka kama mutane 69 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin watan.
“Mutane 10 da ake zargin ’yan fashi da makami ne, mutum tara kuma ana zargin su da aikata laifin kisan kai, 33 da ana zargin su da aikata fyade, luwadi, sauran 26 kuma ana zargin su da laifuka daban-daban.
“Kuma, rundunar ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga takwas, ta kubutar da sama da mutane 87 da aka sace, tare da kwato dabbobi 150d da aka sace,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp