An saki Pavel Durov, mamallakin kafar sadarwa ta Telegram, daga hannun ‘yansanda a Faransa, amma zai ci gaba da fuskantar shari’a yayin da ake ci gaba da tuhumarsa da laifuka masu girma.
Durov, wanda aka haifa a Rasha kuma yana da shaidar zama dan kasar Faransa, an kama shi a filin jirgin sama na Le Bourget bisa zargin da ya shafi ayyukan laifi da ake gudanar da su a Telegram, ciki har da hada kai wajen ba da damar haramtacciyar cinikayya ga kungiyoyin masu laifi.
- ‘Yan Siyasar Nijeriya Ne Ke Ta’azzara Rashin Tsaro Don Cimma Wata Manufa Ta Siyasa – Shugabar WTO
- An Bude Baje Kolin Manyan Bayanai Na Kasa Da Kasa A Kasar Sin
A cikin sharudan sakin Durov dole ne ya biya dala miliyan biyar a matsayin kudin beli, sannan ya kai kansa ofishin ‘yansanda sau biyu a mako, kuma an hana shi barin Faransa.
Binciken da ake gudanarwa game da rawar da Telegram ke takawa a ayyukan laifuka daban-daban, irin su raba hotunan cin zarafin yara ta Intanet, fataucin miyagun kwayoyi, da kuma laifukan kiyayya ta yanar gizo.
Duk da suka da wasu kasashe suka yi, hukumomin Faransa sun jaddada cewa kama Durov wani bangare ne na tabbatar da tsaro.
Telegram ya musanta duk wani laifi, yana mai cewa rashin dace ne a dora wa manhajar ko kuma wanda ya kafa ta alhakin abin da masu amfani da ita suka aikata.
Shari’ar na da rikitarwa, kuma idan aka same shi da laifi, Durov na iya fuskantar hukuncin da zai kai daurin shekaru 10 a gidan yari.