Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama karin wasu mutane uku da ake zargi da yin kalaman batanci ga Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, Usaini Gumel, ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.
- ‘Yansanda Sun Kama Direban Mota Da A-47 Guda 4 A Kano
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 96 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Kano
Tun da farko rundunar ta yi nasarar kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a lamarin.
CP Gumel, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka; Abdulrazak Usman Sarki daga Disu Quarters, karamar hukumar Gwale, sai wani mai suna Fatihu Muktar Faruk Kano da kuma Usman Baba Attah, 25, mazaunin unguwar Kabara Quarters, Kano Municipal.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp