Kwamishinan ‘yansandan Jihar Ribas, Okon Effiong, ya bayar da umarnin binciken harin da aka kai gidan shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Sanata Lee Maeba.
Effiong, a martaninsa a kan harin, ya ce, tuni ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yansanda da ke kula da sashen gudanar da bincike (SCID) da ya yi cikakken bayani kan lamarin.
- Miji Ya Hallaka Matarsa A Kan Ruwan Sha A Legas
- Sahihanci Da Imani Da Goyon Baya Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa
Kwamishinan ya bayyana cewa, “Na bayar da umarnin a gudanar da bincike, inda kuma mataimakin kwamishinan na ‘yansanda da ke kula da sashen gudanar da bincike (SCID) zai yi karin haske a kan lamarin”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp