‘Yansanda a Burkina Faso sun kashe mayakan Islama 40, in ji rundunar a ranar Lahadi.
Rundunar ‘yan sandan kasar ta sanar da cewa ‘yan ta’addar sun yi wa tawagar ‘yan sandan leken asiri a lardin Koulpelogo da ke arewa maso gabashin kasar a ranar Asabar.
- Burkina Faso Da Mali Za Su Tura Tawagar Sojoji Zuwa Nijar
- Juyin Mulki: Kasashen Burkina, Guinea Da Mali Sun Yi Barazanar Taimakawa Nijar Kan Yaki Da ECOWAS
An kuma kashe ‘yan sanda biyar a yayin harin.
Kungiyoyin me dauke da makamai sun shafe shekaru suna fafutuka a jihar Sahel da makwabtanta Mali da Nijar.
Wasu daga cikin kungiyoyin da ke dauke da muggan makamai sun lashi takobin yin mubaya’a ga kungiyoyin ‘yan ta’adda na IS da al-Qaeda.
Dubban mutane ne suka mutu a rikicin da ake yi da kungiyoyin tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.
Dukkanin kasashen uku na karkashin jagorancin shugabannin soji da suka karbi mulki a juyin mulkin soja na baya-bayan nan a Nijar a ranar 26 ga watan Yuli.
Burkina Faso wacce ke da al’umma kusan miliyan 21, gwamnatin rikon kwarya ta soja ce ke jagorantar al’ummar kasar bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.