Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi nasarar kubutar da wata budurwa da aka yi garkuwa da ita daga gidan iyayenta na tsawon kwanaki 30.
Budurwar mai suna Hafsat ‘yar shekaru 20, an kubutar da ita daga hannun wadanda suka yi garkuwa da ita a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.
- An Gudanar Da Taron Ministoci Na Dandalin FOCAC Karo Na 9 A Beijing
- Hadin Gwiwa Ce Tsakanin Sin da Afirka Ba Mulkin Mallaka ba
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa bidiyon ceto budurwar a shafinsa na Facebook.
Kiyawa ya yi cikakken bayanin yadda sashin yaki da masu garkuwa da mutane karkashin CP Aliyu Muhd Auwal suka yi gaggawar karbar rahoton sace budurwar.
An yi garkuwa da Hafsat ne a daren ranar 17 ga watan Agusta, 2024, inda wasu ‘yan bindiga su 10 suka kai farmaki gidan mahaifinta da ke Zarewa, a karamar hukumar Rogo a jihar Kano. Mahaifin ta ya ce, “Sun shiga gidan da tsakar dare, suka yi min dukan tsiya, sannan suka tafi da ‘ya ta.”
Ya bayyana cewa, “masu garkuwar sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 30, ni kuma bani da wadannan kudaden, hakan ya sa na gaggauta sanar da ‘yansanda.”
Bayan wannan rahoto ne rundunar ‘yansandan ta zage damtse inda ta fara bibiyar masu garkuwar har zuwa Makarfi a jihar Kaduna.
Yunkurin Jami’an ya yi nasarar kubutar da Hafsat da wata a maboyar ta ‘yan bindigar.