Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta ce ta kama masu laifi 130 da ake zargi da aikata laifuka a watan Nuwamba, 2023.
An samu wadanda suka aikata manyan laifuka guda 81 daga cikinsu an gurfanar da 61 a gaban kuliya.
- ‘Yansanda Sun Kama Barayi 15, Sun Kwato Motocin Sata 20 A Kano
- Kaduna: Muna Neman Afuwar Kisan Masu Maulidi – Hafsan Sojin Kasa
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abubakar Sadiq Aliyu ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida kan irin nasarorin da rundunar ke samu a kowane wata wajen yaki da miyagun laifuka.
Ya ci gaba da cewa, “A watan sa ya wuce an samu jimillar laifuka kusan 81 da suka hada da manyan laifuka kamar fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai, satar shanu da sauransu, sannan an kama mutane 130 da ake zargi da hannu a cikin lamarin, kuma an gurfanar da mutane 63 a kotu.
“Mutane 38 da ana zargin ‘yan fashi da makami ne, 16 ana zargin su da kisan kai, 19 da ana zargin su da aikata fyade.
“An kama daya da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi sai kuma mutane 42 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban kamar su, cin zarafi, tayar da hankali da dai sauransu.
Aliyu ya kara da cewa rundunar ta kuma yi nasarar ceto mutane 69 da aka yi garkuwa da su, tare da kashe wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da kwato harsashi 185.
“Kwamishanan ‘yansanda ya yaba da kokarin mutanen jihar tare da kara yin kira gare su da su ci gaba da bai wa rundunar goyon baya don yaki da laifuka a jihar”, in ji shi.