Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Theo Walcott ya ce yana ganin wannan ne lokaci mafi dacewa da kungiyar ta arewacin Landan za ta lashe gasar Zakarun Turai ta Tsohon dan wasan na Ingila ya bayyana haka ne yayin da suke sharhi bayan wasan da Arsenal din ta doke Real Madrid 2-1 a wasan zagayen kwata-fayinal ranar Laraba, inda ta fitar da ita daga gasar da ci 5-1 gida da waje kuma yanzu za ta kara da PSG a zagayen kusa da na karshe.
A tarihi dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ba ta taba lashe gasar ba ta Zakarun Turai, sai dai a shekara ta 2006 ta je wasan karshe amma kuma ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Barcelona a wasan da aka fafata a birnin Paris din kasar Faransa.
- Masana’antun Nijeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 1.11 Wajen Samun Wutar Lantarki A 2024 – Rahoto
- ‘Yan Sama Jannati 3 Na Kumbon Shenzhou-20 Na Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniyar Sin Cikin Nasara
“Ina ganin wannan ne lokaci mafi dacewa su ci gasara kofin Zakarun Turai, amma kuma fa za su hadu ne da kungiyar da ke murmurewa tana kara kyau, kuma take a wurin da ya dace, sai dai idan har za su iya doke Real Madrid, to za su iya cin kowa,” in ji Walcott.
Karo na hudu kenan da Arsenal ta kara da Real a kofin Zakarun Turai, inda ta ci uku aka yi canjaras daya. A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karbi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako daya bayan haka. Kungiyar dai ita ce a mataki na biyu a kan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila inda a wannan satin ake saran Liberpool za ta zama zakara a bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp