Rahotonnin da aka yada na cewa dakataccen mataimakin shugaban ‘yan sanda DCP, Abba Kyari na cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje, Abuja a daren ranar Talata ba gaskiya ba ne.
Wani babban jami’in hukumar kula da gidajen yari a Nijeriya, NCoS, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa ‘yan ta’addan da suka kai harin sun yi kokarin fasa dakin kulle da Kyari yake ciki amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Idan za ku iya tunawa dai, a daren ranar Talata ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari gidan yarin Kuje tare da tayar da bam-bamai tare kuma da dauke da muggan makamai.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa bayan Kyari akwai wasu fitattun mutane da suke tsare a gidan yarin da suka hada da tsohon gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyame, da Farouk Lawan, tsohon mambar Majalisar wakilai.
Kazalika, babban sakataren ma’aikatar kula da harkokin cikin gida, Dakta Shuaib Belgore, ya ce sama da fursunoni 600 ne suka arci na kare sakamakon balle gidan yarin da ‘yan ta’addan suka yi.
Ya kuma ce, an sake kamo 300 daga cikinsu, ya kuma ce 300 har yanzu ba a san inda suke ba.