Nasir Almaliky Kabara, kamar dai ya yi amai ya lashe, inda ya bayyana a wani faifan bidiyo yana ikirarin cewa, su Daliban Malam Abduljabbar Sheik Nasir Kabara sun kulla yarjejeniya da Abba Gida-gida kan sako malamin na su da zarar ya dare kujerar Gwamnatin jihar Kano.
Wannan bayanin nasa ya razana masoyan dan takarar da dama a jihar, inda wasu da dama suka shawarci dan takarar da ya fito fili ya yi wa magoya bayansa karin haske kan wannan ikirarin.
Amma daga bisani, Nasir Almaliky Kabara ya sake bayyana a wani faifan bidiyon inda yake neman yafiya kan wancan kalaman nasa.
In ba a manta ba dai a baya, Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a jihar Kano, ta yanke wa Malam Abduljabbar Nasir Kabara hukuncin kisa sabida kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp