Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu dalibai hudu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi a kan hanyar Akunnu-Ajowa da ke yankin Akoko a jihar Ondo a ranar Juma’a.
Daliban, wadanda aka ce suna kan hanyarsu ta komawa gida domin yin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, yankin da ya shahara wajen aikata laifuka, musamman masu garkuwa da mutane.
Ayyukan ta’addanci na sace-sacen mutane a Nijeriya na neman zama ruwan dare a fadin kasar, lamarin da yake neman gagarar gwamnati da Jami’an tsaro, a gefe guda kuwa kan jefa Jama’a cikin damuwa da fargaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp