Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, ana fargabar kusan kimanin mutane 670 ne suka nutse a zaftarewar kasa a sabuwar kasar Guinea (Papua).
Shugaban Hukumar Kula da Hijira ta Duniya a Papua, Serhan Aktoprak, ya ce, zaftarewar kasa da aka yi a ranar Juma’a a lardin Enga da ke kasar ya wuce yadda aka yi hasashe tun farko.
- Ina Nan A Matsayin Sarkin Kano, Har Sai Na Ga Umarnin Kotun – Sanusi II
- Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde Ya Rasu
“Akwai kiyasin gidaje fiye da 150 da suka rufta,” in ji Mista Aktoprak.
A cewar jami’in, yankunan da lamarin ya shafa sun kasance a tsaunukan Enga, a arewacin tsibirin da ke kudu maso yammacin tekun Pacific.
Ana kara kai agajin gaggawa domin ceto wadanda bala’in zaftarewar kasa ya rutsa da su a lardin Enga da ke kasar, inda ake fargabar daruruwan mutane sun mutu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp