Rahotanni da ke fitowa a halin yanzu sun nuna cewa, wani bangare na masallacin Fadar Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya rufta a daidai lokacin da mutane yayin da ake gudanar da sallar la’asar.
Ganau a wajen sun bayyana cewa mutane da dama an zakulosu babu rai, yayin da aka garzaya da wasu zuwa asibiti.
Sai dai har zuwa hada wannan rahoto ba a tantance yawan adadin mutunen da suka mutu ba da kuma wadanda suka jikkata.
Muna tafe da karin bayani nan gaba kan batun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp