Yunkurin Nijeriya na karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2027 da Jamhuriyar Benin ya ci tura.
Hakan ya biyo bayan matakin da hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta dauka na bai wa kasashen Kenya da Uganda da Tanzania damar daukar nauyin gasar.
- Rashford Ya Yi Hatsarin Mota A Hanyarsa Ta Zuwa Gida Bayan Tashi Daga Wasansu Da Burnley
- Sadio Mane Ya Koma Kungiyar Al Nassr Daga Bayern Munich
CAF ta bayyana hakan ne a karshen taron kwamitin zartarwa da ta gudanar a ranar Laraba.
Kasar Morocco ce ta samu nasarar daukar nauyin gasar ta AFCON a shekarar 2025.
Nijeriya ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa mafi girma a Afirka a shekarar 2000.
Kasar ta dauki nauyin gasar ne tare da kasar Ghana a waccan shekarar.