Sabon dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta AL Nassr, Sadio Mane ya jinjinawa takwarsan Cristiano Ronaldo kan jefa kwallo da ya yi a ranar Alhamis.
Mane ya raba gari da Bayern Munich bayan shafe kakar wasa daya da kungiyar.
- Ronaldo Ya Jefa Kwallon Da Ta Saka Kungiyarsa Zagayen Gaba A Gasar Zakarun Larabawa
- Juyin Mulki: Yadda Amfani Da Karfin Soja A Kan Nijar Zai Shafi Nijeriya —Masana
Kocin kungiyar, Luis Castro ya fara wasan da Mane a matsayin dan canji, wanda bayan sako shi a wasan ya kasa katabus, sai Ronaldo ne ya fitar da Al Nassr kunya.
Talla
Mane ya yabawa Ronaldo dan shekara 38 a duniya a shafinsa na Instagram kan bajintar da ya yi.
Kwallon da Ronaldo ya zura ita ce kwallonsa ta 840 da rayuwarsa ta kwallon kafa baki daya.
Talla