A ranar Laraba ne shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin Nijeriya ta kasa da ta sama da jamhuriyar Benin tare da dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar ta ce, umarnin ya yi daidai da matsayar da kungiyar ECOWAS ta cimma a babban taronta na musamman da ta yi a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja.
- Juyin Mulki: Sojojin Nijar Sun Fara Shirin Sakin Shugaba Bazoum
- ECOWAS Ta Cire Takunkuman Da Ta Kakaba Wa Kasashen Nijar, Mali Da Guinea-Bissau
Sanarwar ta ce, “Shugabannin ECOWAS sun amince da dage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.”
Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarnin dage takunkuman da aka kakaba wa Jamhuriyar Nijar cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp