Wasu rahotanni na nuna yiwuwar sojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar za su iya amincewa da sakin hambrarren shugaban kasar, Mohamed Bazoum da iyalinsa kowanne lokaci daga yanzu.
Rahotannin sun bayyana cewar akwai yiwuwar cimma matsaya kan sakin shugaban a cikin watan Ramadan.
- Gobara Ta Hallaka Yara 2 A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Borno
- Za Mu Iya Afmani Da Watan Ramadan Wajan Magance Matsalolin Da Muke Ciki – Fintiri
A cewar bayanan har yanzu akwai dambarwar dangane da bukatar Bazoum ya ci gaba da zama a Nijar ba tare da fitarsa kowace kasa ba, wanda shi ne dalilin da ya kai ga gaza sakinsa har a wannan lokaci.
Bazoum dai na samun cikakken goyon bayan shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS).
Hakan ya sa ana ganin shi ya sake tsaurara matakan sakin nasa daga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.
Tun bayan hambarar da gwamnatin ta Bazoum Mohamed a watan Yulin 2023, Nijar ta fuskanci takunkumai daga Faransa da ECOWAS, lamarin da zafafa alaka tsakanin Nijar da Nijeriya.
Baya ga Nijar ECOWAS ta kuma kakaba wa Mali da Burkina Faso wadanda ke fuskantar mulkin soji, takunkumai.